Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Batun kasar Sin ta nemi gafara ma bai taso ba
2020-03-05 21:10:11        cri

"Matakin bata suna ya fi cutar ma tsoratarwa. Bari in kara jaddada cewa, matakin bata suna shi ne babban abokin gaba mafi tsoratarwa." Babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka shirya a kwanan baya, inda ya nuna bakin cikinsa kan yadda ake neman bata suna a yayin da ake yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

A matsayinta na kasar da aka fara gano annobar, kasar Sin ta fi fuskantar irin wannan hali na neman bata sunanta. A 'yan kwanakin da suka wuce, wani mai gabatar da shiri a gidan talibijin na Fox na kasar Amurka ya ce wai "Kwayar cutar numfashi ta COVID-19 ta samo asali ne daga kasar Sin", kuma ya nemi kasar Sin ta nemi gafara a hukunce.

To, bari mu tambayi wannan mai gabatar shirin: annobar murar H1N1 da ta bulla a shekarar 2009 a kasar Amurka, ta kuma yadu zuwa kasashe da shiyyoyi 214, wadda ta haddasa rasuwar mutane kusan dubu 300 a daukacin duniya, wa ya fadawa Amurka ta nemi gafara? Yanzu, ba a iya tabbatar da asalin cutar ba, kamar sauran kasashen da annobar ta shafa, kasar Sin ce ma ta tafka hasara sanadiyar cutar.

Kwanan baya, tawagar kwararrun Sin da WHO ta ba da rahoton binciken da ta gudanar cewa, kasar Sin ta dauki matakai mafi jarunta da sauki kuma mai yakini don kandagarki da shawo kan wannan cutar da ba a taba sani ba, matakai da suka taimakawa a kalla mutane dubu 100 hana kamuwa da cutar, ta yadda aka kafa tsarin kandagarki na farko na hana yaduwar annobar a tsakanin kasa da kasa.

A yayin da yake zantawa da wakilan gidan talibijin na CGTN mallakar babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, shugaban tawagar WHO Bruce Aylward ya kara nuna cewa, dole ne a girmama nasarorin da kasar Sin da jama'arta suka samu, musamman ma a wannan yanayi na gaggawa na tinkarar annobar, "Kasar Sin ta nuna misali ga duniya baki daya".

Yanzu wannan sabuwar cutar da ba a san asalinta ba, abokiyar gabar daukacin dan Adam ne. A cikin wannan lokaci da duniya ke kokarin dunkulewa waje guda, hadin kai shi ne makami mafi karfi wajen yaki da annobar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China