Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahohin Sin na yaki da cutar COVID-19 za su ci gaba da ba da gudummawa ga gamayyar kasa da kasa
2020-03-05 13:09:59        cri

A halin yanzu da ake fuskantar hadarin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 cikin wasu kasashen duniya, sakamakon da kasar Sin ta cimma wajen hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ya fara samun amincewa da yabo daga gamayyar kasa da kasa. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta yi mu'amala da gamayyar kasa da kasa kan harkokin kandagarki da na samar da jinya cikin sauri, lamarin da ya baiwa sauran kasashen duniya lokaci da damar shiryawa wajen yaki da annobar, ya kuma kara imanin gamayyar kasa da kasa wajen cimma nasarar yaki da annobar.

Matakan da kasar Sin ta dauka wajen hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 sun kawo hasarar tattalin arzikin kasa, da haddasa wasu matsaloli ga zaman rayuwar al'ummar kasa, lamarin da ya matsawa al'ummomin kasar lamba sosai. Wannan ya zama jarrabawar da aka yi kan karfin mulki na gwamnatin kasar Sin, da kuma karfin al'ummomin kasar na yin kamun kai. A karshe dai, kasar Sin da al'ummarta sun cimma wannan jarrabawa.

Hukumar lafiyar duniya ta WHO ta jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su mai da aikin hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a matsayin muhimmin aikin dake gabansu, da daukar matakai cikin sauri domin hana yaduwar cutar. Kana, fasahohin kasar Sin za su samar wa kasa da kasa goyon baya, tabbas ne za a cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China