Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wane sako masanan kasa da kasa suka isar dangane da matakan kandagarkin cutar COVID-19 da kasar Sin ta dauka?
2020-03-01 20:18:43        cri

Rahoton bincike na hadin gwiwa wanda kasar Sin da hukumar lafiya ta duniya(WHO) suka gudanar dangane da cutar numfashi ta COVID-19, wanda aka fitar a jiya Asabar ya yi nuni da cewa, "Kasar Sin ta dauki matakan da suka fi nuna jajurcewa da inganci a tarihi". Masana 25 da suka zo daga kasashen Sin da Jamus da Japan da Koriya ta Kudu da Nijeriya da Rasha da Singapore da Amurka da WHO ne suka cimma daidaito bayan da suka shafe kwanaki 9 suna gudanar da bincike a kasar Sin.

Rahoton ya ce, kasar Sin ta dauki kwararan matakai daga fannoni daban daban, wadanda suka katse hanyoyin yaduwar cutar. Ban da haka, kasar Sin ta kuma yi amfani da fasahohin zamani da suka hada da kwaikwayon tunanin dan Adam da fasahar 5G da sauransu wajen warkar da mutanen da suka kamu da cutar. Baya ga haka, kasar Sin ta kuma samar da dimbin na'urorin kiwon lafiya tare da tura ma'aikatan lafiya sama da dubu 40 zuwa lardin Wuhan. Haka kuma al'ummar kasar Sin baki daya sun hada kansu wajen samar da gudunmawar kayayyaki ga lardin Wuhan. Duk wadannan sun burge masanan kwarai da gaske.

Kwalliya tana biyan kudin sabulu, kasar Sin ta fara samun saukin yanayin cutar. Duk da haka, cutar na yaduwa a sassa daban daban na duniya. Aikin da ya kamata kasa da kasa suka sanya a gaba shi ne su gaggauta daukar matakan dakile yaduwar cutar. Rahoton ya kuma jaddada cewa, matakan da kasar Sin ta dauka sun samar da darasi ga kasa da kasa wajen tinkarar cutar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China