Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karin mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a jiya ya kai 125 a babban yankin kasar Sin
2020-03-03 11:16:22        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce a jiya Talata, karin mutane da suka kamu da cutar COVID 19 a babban yankin kasar ya kai 125, sannan karin mutane 31 sun mutu sakamakon cutar. Hukumar ta kara da cewa, karin mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ya kai 129, sannan karin mutanen da suka warke daga cutar ya kai 2742.

Hakan ya sa, zuwa karshen ranar Litinin, yawan mutanen da suka kamu da cutar gami da wadanda suka taba kamuwa da cutar a babban yankin kasar ya kai 80151, yayin da yawan mutanen da ake zaton sun kamu da cutar yanzu ya kai 587. Haka kuma yawan mutanen da suka warke daga cutar ya kai 47204, yayin da mutanen da suka rasu sakamakon cutar ya kai 2943.Adadin wadanda aka kebe don sa ido kuma ya kai 40651. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China