Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta damu matuka da karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a yankin gabashin Bahr Rum
2020-03-04 10:38:04        cri

Bisa rahoto na baya-bayan nan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar game da cutar numfashi ta COVID-19, ya zuwa karfe 10 na safiyar jiya agogon Turai, jimillar adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 10,566 a kasashe 72 ban da kasar Sin, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 166.

Idan aka kwatanta da rahoton da hukumar ta fitar a ranar Litinin, an samu karuwar mutane 1,792 da suka kamu da cutar a wajen kasar Sin, sannan an samu karin kasashe 8 da cutar ta bulla, da suka hada da Andorra da Jordan da Latvia da Morocco da Portugal da Saudiyya da Senegal da kuma Tunisia, inda addin sabbin wadanda suka mutu ya kai 38.

WHO ta kuma bayyana damuwa matuka, game da karuwar masu kamuwa da cutar a yankin gabashin tekun Bahr Rum, inda Daraktan hukumar a yankin ya jaddada bukatar karfafa sa ido da ayyukan tunkarar cutar da musayar bayanai domin dakile yaduwarta da karfafa tsarin ayyukan kiwon lafiya. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China