Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyun siyasa na ketare da hukumomin kasa da kasa na da karfin gwiwa kan kwazon kasar Sin na kawo karshen COVID-19
2020-02-28 20:48:38        cri

Shugabannin jam'iyyun siyasa na kasashen ketare, da hukumomin kasa da kasa daban daban na ci gaba da nuna karfin gwiwarsu, ga irin kwazon kasar Sin na shawo kan cutar numfash ta COVID-19. Sassan sun bayyana hakan ne, cikin wani sako da suka aike ga ofishin sashen harkokin kasa da kasa na kwamitin kolin JKS.

Faysal Hassan Ibrahim, shi ne babban sakataren kungiyar jam'iyyun siyasun nahiyar Afirka, ya kuma bayyana cikakken goyon bayansa ga matakan yaki da cutar da kasar Sin ke aiwatarwa. Ibrahim ya bayyana hakan ne, a madadin kasashen Afirka 34, da kuma jam'iyyun siyasar nahiyar 45.

A nasa bangare, shugaban jam'iyyar "European Left" Heinz Bierbaum, cewa ya yi, tuni Sin ta aiwatar da matakan dakile yaduwar cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China