Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
EU na darajta matakin da Sin ke dauka wajen yaki da cutar COVID-19
2020-02-28 20:17:38        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Juma'a cewa, Sin na godiya da goyon baya mai daraja, da bangarori daban-daban, ciki hadda kawancen tarayyar Turai na EU ke nuna wa kasar, game da aikin yaki da cutar COVID-19.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa, game da sanarwar da EU ta bayar, bayan taron kwamitin hadin kai kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da aka yi kwanan baya, inda EUn ta yi matukar darajta muhimmiyar gudunmawar da Sin take bayarwa, wajen tinkarar matsalar kiwon lafiya a duniya.

Zao Lijian ya kara da cewa, wannan mumunar cuta na iya yaduwa a duk fadin duniya, kuma Sin na mai da hankali sosai kan nahiyar Turai, da kuma Iran, don ganin yadda za a magance wannan cutar, kuma tana fatan kara hadin kanta da sauran kasashen duniya, don tinkarar wannan matsalar kiwon lafiya ta kasa da kasa tare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China