Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban WHO ya yi kira da a samar da karin kayayyakin kariya daga cutar COVID-19
2020-03-04 10:19:20        cri

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Mr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi kira ga dukkanin sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen samar da kayayyakin da ake amfani da su, domin kare kai daga kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19, domin biyan bukatun al'ummar duniya, musamman a wannan gaba da cutar ke kara bazuwa zuwa karin kasashen duniya.

Ghebreyesus wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na jiya Talata, ya ce bisa kiyasi, ana bukatar karin kaso 40 bisa dari na irin wadannan kayayyakin kariya a duniya baki daya, kuma karancin safar hannu ta kariya, da abun rufe baki da hanci, da na'urar taimakawa numfashi, da tabarau na kariya, da abun rufe fuska, na jefa jami'an lafiya cikin hadarin kamuwa da cutar, yayin da suke kula da masu dauke da ita.

Jami'in ya ce, bisa kiyasin hukumar WHO, a duk wata, ana bukatar abun rufe baki da hanci miliyan 89, da safar kariya ta hannu miliyan 76, da tabaran kariya miliyan 1.6, duka dai domin aikin kandagarkin yaduwar cutar ta COVID-19.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China