Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a wajen kasar Sin ya kai 8774
2020-03-03 13:24:28        cri

Alkaluman kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar a jiya, sun nuna cewa ya zuwan karfe 10 na safe agogon Turai, kasashe 64 a duniya ban da kasar Sin sun samu mutanen da suka kamu da cutar 8774, kuma yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai 128. Idan aka kwatanta da rahoton da ta gabatar a ranar Lahadi, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da 1598, karin kasashen da suka gano wannan cutar su ne Armenia, Czech, Dominica, Luxembourg, Iceland, da Indonesia.

Ya zuwa karfe 6 da yammacin ranar 2 ga wata, yawan mutanen da suka kamu da cutar a Italiya ya kai 2036, kuma kasar dai ta gudanar da aikin gwajin kwayoyin cuta kan mutane 23300.

Ban da wannan kuma, ya zuwa karfe 9 na daren ranar 2 ga wata, yawan mutanen da suka kamu da cutar a Japan ya kai 980, ciki hadda Japanawa da suka kamu da cutar a cikin kasar da kuma masu yawon bude ido Sinawa 260, da kuma fasinjoji da ma'aikatan jirgin ruwan mai suna "Diamond princess" 706, da kuma Japanawa 14 wadanda suka koma kasar ta jirgin sama na musamman da gwamnatin kasar ta tura. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China