Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya ya yi alkawarin baiwa kananan da matsakaitan masana'antun Afirka Karin rance
2020-02-14 11:44:10        cri
Babban bankin duniya, ya yi alkawarin baiwa kananan da matsakaitan masana'antun Afirka (SMS) Karin rance. Masaniyar sashen kudi na bankin Luz Maria Salamina ce ta bayyana hakan yayin taron dandalin kula da harkokin rance karo na biyar na shekarar 2020 da ya gudana a birnin Nairobin Kenya.

Ta ce babban kalubalen da kanana da matsakaitun masana'antu ke fuskanta shi ne, samun rance, duk da rawar da suke takawa a fannin bunkasar tattalin arziki.

A cewar ta, bankin zai bullo da tsare-tsaren da za su taimakawa nahiyar yiwa dokokinta gyaran fuska, ta yadda za ta ci gajiyar irin wadannan rance, da magance hadarin da masu ajiyar kudade za su iya fuskanta.

Don haka ta bukaci kasashen nahiyar, da su tabbatar cewa,kanana da matsakaitan masana'antu sun samu damar karbar rance da ya dace, duba da irin dimbin guraben ayyukan yi da za su samar.

Manufar taron na kwanaki biyu wanda ya hallara wakilai daga manyan bankunan kasashen Afirka 15,da sashen raya harkokin kudi,da kungoyoyi masu zaman kansu,da bankunan kasuwanci da hukumomin ba da rance, ita ce auna ci gaban da nahiyar ta samu a fannin kasuwannin ba da lamuni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China