Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Wajibi ne MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da tunanin kasancewar sassa daban daban a duniya
2019-10-23 13:28:52        cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Switzerland Ignazio Cassis sun gana da manema labaru a jiya Talata, inda Wang Yi ya ce, ranar 24 ga wata, rana ce ta MDD, kuma ya dace a yi amfani da wannan rana, a yi bitar muhimman ka'idojin kundin tsarin MDD, a bi manyan ka'idojin tinkarar huldar da ke tsakanin kasa da kasa, da hada kai wajen yaki da daukar matakin gashin kai da cin zali, da kuma kokarin kiyaye martabar MDD da matsayinta.

Wang Yi ya kara da cewa, wajibi ne MDD ta yi tafiya daidai da zamani, ta yi ta kyautata kanta. La'akari da cewa yawancin kasashen da suka shiga MDD bayan babban yakin duniya na 2, kasashe ne masu tasowa, kamata ya yi MDD ta girmama matsayin kasashe masu tasowa, da kiyaye halaltattun hakkokinsu.

Babban jami'in na kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin ta zama ta farko da ta sa hannu kan kundin tsarin MDD, inda ya ce a matsayinta na wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu, kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin da kasashen duniya suke dora mata, za ta kuma hada kai da kasashen duniya wajen kiyaye tsarin kasa da kasa, karkashin ka'idojin da dokokin MDD. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China