Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Martin Chungong: ba za a iya warware matsalolin kasa da kasa ba, sai a warware su tsakanin sassa daban daban
2020-01-19 16:08:28        cri

A gabanin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na shekarar 2020 a Davos, Martin Chungong, babban sakataren kawancen majalisun kasa da kasa wato IPU ya jaddada cewa, yanzu kasashen duniya na fuskantar matsaloli da dama, ba za a iya warware su ba, sai idan an fara warware matsalolin a tsakanin sassa daban daban.

A yayin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, Martin Chungong ya yabawa jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taro tsakanin manyan jami'ai dangane da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama a Geneva a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2017. Ra'ayin Xi Jinping na raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama ya aza harsashi mai inganci wajen warware matsalolin da kasashen duniya ke fuskantar a halin yanzu.

Chungong ya kara da cewa, yanzu kasar Sin tana samun saurin ci gaba. Amma ba ta son ganin ita kawai ta samu ci gaban, tana fatan samun wadata tare da sauran kasashen duniya. Wannan shi ne dalilin da ya sa ya jinjinawa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, shawarar wacce za ta kara azama kan hadewar duniya baki daya, ta haka za a hada kai domin samun nasara tare.

Chungong ya ci gaba da cewa, duniyarmu, gidan kowa da kowa ne. Ya zama tilas a gudanar da aikin raya ci gaba kafada da kafada, domin cin gajiyar sakamakon da aka samu ta hanyar yin kokari tare. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China