Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WEF: Kasashen duniya na bukatar hada kai wajen tinkarar barazana
2020-01-16 10:19:19        cri

Jiya Laraba 15 ga wata a birnin London taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya wato World Economic Forum ko kuma WEF a takaice ya kaddamar da rahotonsa kan barazanar da kasashen duniya za su fuskanta a shekarar 2020, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kansu cikin hanzari wajen rage barazanar da za su tsananta ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma tinkarar kalubalen da matsalar sauyin yanayi ta dade tana kawowa.

Rahoton ya yi hasashen cewa, a shekarar 2020 da muke ciki, ana kara nuna bambanci tsakanin sassa daban daban, kana tattalin arzikin ya kara samun koma baya.

Rahoton ya ci gaba da cewa, a karo na farko barazanar da kasahen duniya za su fuskanta a manyan fannoni guda 5 nan da shekaru 10 masu zuwa za su shafi yanayin muhalli duka. Mutanen da aka ji ra'ayoyinsu suna ganin cewa, tsananin zafi ko sanyi da dai makamantansu, gazawa wajen daukar matakan magance matsalar sauyin yanayi, munanan bala'u daga Indallahi, karancin kasancewar halittu iri daban daban a duniya da tabarbarewar tsarin yanayin halittu, da gurbata muhalli su ne barazanar da suka fi yiwuwar abkuwa, kuma za su fi yin illa a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China