Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Senegal ta tabbatar da bullar cutar COVID-19 na farko
2020-03-03 10:04:18        cri

Ministan lafiya na kasar Senegal, Abdoulaye Diouf Sarr, ya tabbatar da bullar cutar numfashi ta COVID-19 na farko a kasar a jiya Litinin.

Abdoulaye Diouf Sarr, ya ce wanda ya harbu da cutar dan kasar Faransa ne mai yara 2, wanda ya koma Dakar daga Paris a ranar 26 ga watan Fabrairu, bayan ya yi hutu a yankin kudancin Faransa.

A ranar 28 ga watan Febrairu ne, wani asibiti mai zaman kansa, ya sanar da hukumomin lafiya na kasar game da mara lafiyan da ya nuna alamun cutar COVID-19.

Gwajin da aka yi masa a cibiyar binciken cututtuka da kwayoyin halitta ta Pasteur dake Dakar ne ya nuna yana dauke da cutar, sai dai baya cikin yanayi mai tsanani. Baya ga haka, an killace iyalansa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China