![]() |
|
2019-06-25 14:27:38 cri |
Malick Diop, shugaban hukumar kara azama kan sayar da kaya a ketare ta kasar Senegal ya bayyana a kwanakin baya cewa, bikin baje kolin tattalin arziki da ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka karo na 1 da za a gudanar a birnin Changsha na lardin Hunan a kasar Sin ba da dadewa ba, wani muhimmin mataki ne da aka dauka domin aiwatar da manyan ayyuka 8 karkashin tsarin taron dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, inda kasashen Afirka da dama za su halarta, ciki har da kasarsa ta Senegal, wadda ke matsayin babbar bakuwa ta bikin, lamarin da yake da muhimmiyar ma'ana.
Mista Diop ya yi imanin cewa, bikin zai kasance wata kyakkyawar dama ta kara sayar da kayayyakin kasarsa a kasar Sin. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China