Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Senegal
2019-12-21 16:04:56        cri

Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kana direktan ofishin kwamiti mai kula da harkokin diflomasiyya na kwamitin tsakiyar JKS, Yang Jiechi, ya gana da shugaban kasar Senegal Macky SALL kwanan baya a Dakar, fadar mulkin kasar.

Yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya ce, Senegal ce kasa ta farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara a yammacin Afrika. Shugabannin biyu sun gana da juna sau da dama tare da cimma matsaya kan wasu manyan batutuwa, matakin da ya ingiza bunkasuwar dangantakar kasashen biyu. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu suna yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ciki har da ayyukan shimfida manyan hanyoyin mota da haka rijiyoyi a kauyuka da dai sauransu, matakan da suka amfanawa tattalin arziki da al'ummar kasar sosai. Sin tana goyon bayan tsarin da Senegal ke dauka na farfado da kasar, da kuma karbar bakuncin bikin wasannin motsa jiki na matasa na shekarar 2022, Sin tana fatan kyautata hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin samar da muhimman ababen more rayuwa da bunkasa masana'antu da sauransu, har ma da karawa kamfanonin kasashen biyu kwarin gwiwa ta fuskar hadin kansu a fannoni daban-daban.

A nasa bangare, Macky Sall ya ce, kasashen biyu suna amincewa da juna matuka, har ma sun dade suna baiwa juna taimako da goyon baya, matakan da ya kai ga dangantakar kasashen biyu ta abota bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi. Senegal tana kara nacewa ga shawarar "Ziri daya da hanya daya". Shirin kasar Sin na yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga ketare ya jawo hankalin kasashen duniya sosai, lamarin da ya baiwa nahiyar Afrika fasaha mai kyau wajen bullo da wata hanyar samun bunkasuwa da ta dace da halin da nahiyar ke ciki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China