Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Senegal ya bayyana goyon bayansa ga kasar Sin
2020-02-05 17:24:14        cri

A kokarin da kasar Sin ke ci gaba da gudanarwa na yaki da annobar cutar numfashin ta coronavirus, jami'an lafiyar kasar sun daura damarar dakile yaduwar sabuwar kwayar cutar.

Kawo yanzu, kasar Sin tana ci gaba da samun yabo da taimako da goyon baya daga kasashen daban daban na duniya a yakin da take yi da annobar.

A Senegal, shugaban kasar Macky Sall ya bayyana cikakken goyon bayan kasarsa ga kasar Sin, kana ya yabawa irin matakan da kasar Sin ke dauka na ganin ta dakile bazuwar kwayoyin cutar a tsakanin jama'a.

Ya zuwa ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, an samu adadin mutane 716 da suka warke daga cutar. Yayin da mutane 426 suka mutu a sanadiyyar annobar a kasar Sin, sai kuma mutum guda wanda cutar ta kashe a ketare. Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 20,527, yayin da yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a ketare ya kai 176.

Gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da yaki da cutar bisa matakin koli a larduna da birane da yankuna masu cin gashin kai 31 a fadin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China