Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana sa kaimi ga kamfanoni masu kula da aikin gona don su koma bakin ayyukansu
2020-02-29 16:55:57        cri
Yanzu ana kokarin gudanar da ayyukan shuke-shuke a lokacin bazara a wurare daban daban na kasar Sin. Dangane da lamarin, ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ta fidda wata sanarwa a jiya Jumma'a, inda ta bukaci hukumomin wurare daban daban da su yi kokarin samar wa manoma kayayyakin da suke bukata don gudanar da harkokinsu, ta yadda za a tabbatar da gudanar harkar shuka a lokacin bazara, a kuma wannan lokacin da ake kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar.

Ma'aikatar ta bukaci a yi kokarin sa kaimi ga kamfanoni masu samar da kayayyakin da manoma suke bukata don su koma ga gudanar da ayyukansu cikin sauri, da tabbatar da ayyukan samar da rance, da rage haraji da tallafawa wadannan kamfanonin. Sa'an nan za a kyautata fasahar sayar da kayayyakin aikin noma, ta yadda aikin sayar da kayayyakin ba zai gamu da matsala ba a wannan lokaci na musamman. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China