Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta lashi takwabin samar da guraben ayyukan yi
2020-02-28 15:40:00        cri
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na daukar managartan matakan da za su tabbatar da samar da guraben ayyukan yi, ciki har da karfafa gwiwar daukar mutane aiki ta kafar intanet da samar da tallafin kudade ga kananan masana'antu, da daidaita tasirin da annobar COVID-19 ta haifawar bangaren ayyukan yi.

Mataimakin ministan tsaron jama'a You Jun ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai a Jumma'ar nan, Ya ce, tuni aka kaddamar da matakai kamar shirya tarukan baje kolin daukar ma'aikata aiki ta intanet, da samar da horon sanin makamar aiki, don bunkasa muhimman hanyoyin samun aiki, ciki har da daliban da suka kammala karatu a kwalejoji da ma'aikata 'yan ci-rani dake yankunan karkara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China