Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kunbon bincike na kasar Sin ya gano sirrin dake binne a bangaren wata mai nisa
2020-02-27 12:12:42        cri

Kumbon bincike na Yutu-2 na kasar Sin ko Jade Rabbit-2, da kasar Sin ta harba, ya taimakawa masana kimiya gano sirrin dake binne a kasan bangaren wata mai nisa, matakin da ya taimakawa dan-Adam kara fahimtar tarihin duniya da yadda duwatsu ke amon wuta da yin karin haske kan wanzuwar Ilimin duwatsu a duniyar wata.

A ranar 3 ga watan Janairun shekarar 2019 ne, tauraron dan-Adam na Chang'e-4 na kasar Sin ya fara sauka a bangaren duniyar wata mai nisa. Bayan ya sauka ne kuma, ya tura kumbun bincke na Yutu-2, inda ya yi amfani da na'urar Radar(LPR) don gudanar da bincike a karkashin sashe na duniyar wata mai nisa.

Binciken da tawagar masana karkashin jagorancin Li Chunlai da Su Yan suka gudanar a dakin binciken cibiyar kimiya ta kasar Sin(NAOC) ya nuna abubuwan dake binne a duniyar wata.

Masana kimiya sun tantance hotunan da na'urar ta dauka, kuma sakamakon ya nuna cewa, akwai duwatsu iri daban-daban. A yau ne kuma 27 ga wata agogon Beijing na kasar Sin, aka wallafa sakamakon nazarin, kan ci gaban kimiya na baya-bayan da aka samu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China