Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin ilmin numfashi na Sin: watakila asalin cutar COVID-19 ba daga kasar Sin ba ne
2020-02-27 16:12:53        cri
Masanin ilmin numfashi na Sin Zhong Nanshan ya bayyana a yau cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta bullo da farko a kasar Sin, amma watakila asalin cutar ba daga kasar Sin ba ne.

Masanin ya bayyana hakan a gun taron manema labaru da gwamnatin birnin Guangzhou na kasar Sin ta gudanar a wannan rana.

Game da saurin karuwar yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasashen Japan da Koriya ta Kudu, Zhong Nanshan ya bayyana cewa, ya kamata a more fasahohin magance da yaki da cutar, da kara yin hadin gwiwa a wannan fanni. A yayin da Sin ke fuskantar cutar, Japan da Koriya ta Kudu sun nuna goyon baya ga Sin, don haka, ya kamata Sin ta nuna goyon baya gare su.

Zhong Nanshan ya kara da cewa, idan aka duba yanayin faruwar cututtuka masu tsanani a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, an gano cewa kashi 80 cikin dari nasu an same su ne daga dabobbi. Dan Adam da dabobbi suna kara yin zaman rayuwa tare, ta yadda wasu kwayoyin cututtuka dake cikin jikin dabobbi suna iya yadawa zuwa jikin dan Adam. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China