Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ce Sin da Mongolia na taimakawa juna a lokutan da ake tunkarar wahalhalu
2020-02-27 19:41:32        cri

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karbi bakuncin shugaban Mongolia Khaltmaa Battulga, a babban zauren taruwar jama'a dake nan birnin Beijing.

Shugaba Xi ya bayyana ziyarar Mr. Battulga, dake da nufin karfafa goyon baya ga al'ummar Sinawa, a matsayin alamar dake nuni ga martaba alakar kasashen biyu, da shugaban na Mangolia ke nunawa, kaza lika hakan na shaida dankon zumunta dake akwai, tsakanin al'ummun kasashen biyu.

Hailing Battulga, shi ne shugaban wata kasa na farko da ya ziyarci Sin, tun bayan bullar cutar numfashi ta COVID-19. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China