Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: farashin hajojin zai daidaita yayin da ake samar da karin kayayyaki
2020-02-27 20:02:04        cri

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce ba da jimawa ba, farashin kayayyakin amfanin yau da kullum zai daidaita, yayin da karin kayayyaki ke shiga kasuwanni, kuma matakan da gwamnati ke dauka ke kara yin tasiri.

Da yake tsokaci ga manema labarai ta kafar bidiyo game da hakan, jami'in ma'aikatar Wang Bin, ya ce cikin kankanen lokaci, farashin kayayyakin amfanin yau da kullum zai yi sauki, yayin da ake samun karin hajojin da masana'antu ke sarrafawa, kuma manufofin gwamnati da suka hada da rage haraji, da saukaka harkokin ba da hidima ke kara kyautata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China