Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: ya kamata kasa da kasa su kara daukar matakan yaki da cutar COVID-19
2020-02-27 16:20:58        cri
Babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a gun taron karin haske game da yanayin cutar numfashi ta COVID-19 da aka gudanar a birnin Geneva a jiya cewa, akwai wasu alamu masu yakini yayin da ake tinkarar cutar a duniya, wadanda suka shaida cewa, ana iya hana yaduwar cutar, amma ya kamata kasa da kasa su kara daukar matakan yaki da cutar don magance karin yaduwar cutar a duniya.

Tedros ya kara yin bayani game da ra'ayoyin tawagar hukumar ta masana da aka tura kasar Sin, inda ya ce, an kai matsayin koli na karuwar yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin tun daga ranar 23 ga watan Janairu zuwa ranar 2 ga watan Febrairu, daga baya yawansu ya ci gaba da raguwa, kana ba a samu babban canji kan kwayoyin cutar ba, kuma matakan Sin na magancewa da yaki da cutar sun dakile karuwar yawan masu kamuwa da cutar. Ya ce, wannan ya shaida cewa ana iya hana yaduwar cutar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China