Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Kasar Sin ya bukaci kasashen duniya da su kare matakan hana yaduwar makamai da aka cimma
2020-02-27 12:06:46        cri

Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD, Wu Haitao, ya bukaci kasashen duniya, da su kiyaye matakan da aka cimma na takaita yaduwar makamai da kwance damara, tare da nuna adawa da janyewa daga yarjejeniyar da aka cimma da ma keta ta.

Wu ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a taron kwamitin sulhu na MDD game da hana yaduwar makaman nukiliya. Ya ce, dokar hana yaduwar makaman nukliya da aka cimma(NPT), ita ce ginshikin kwance damarar makaman kuliya a duniya da ma tsarin kawar da makaman baki daya daga doron kasa.

Ya ce, bana shekaru 50 ke nan da fara amfani da wannan yarjejeniya, kana shekaru 25 da aka kara fadada ta. Wu ya ce, akwai bukatar mambobin kwamitin sulhun majalisar, su tuna rawar da yarjejeniyar ta cimma a tarihi, su kuma kalli muhimmancinta game da tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

Wakilin na kasar Sin ya kuma yi kira da a karfafa matakan hana yaduwar makaman nukiliya da kawar da duk wata barazana da yaduwar makaman mukiliyar za ta haifar. Ya kara da cewa, ya kamata hukumomi da jami'o'in dake hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa, su karfafa tare da zage damtse wajen yin watsi da nuna wariya da yin fuska biyu kan wannan batu.

Ya ce, kasar Sin ta kudiri aniyar kama turbar tabbatar da zaman lafiya da tsara manufofin ketare masu zaman kansu game da tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa. Haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da shiga alakar kasa da kasa, da martaba dokokin takaita yaduwar makamai na kasa da kasa da matakan hana yaduwar makaman, za kuma ta ba da gudummawa a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga daukacin bil-Adam.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China