Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu Wanda Zai Mayar Da Kasar Sin Saniyar Ware
2020-02-17 20:24:06        cri
A jiya Lahadi 16 ga wata, al'amura guda biyu sun faru, daya daga cikinsu shi ne tawagar kwararrun da kungiyar lafiyar duniya wato WHO ta tura ta sauka a birnin Beijing, dayan kuma shi ne jiragen kasan dakon kayayyaki dauke da manyan kwantenonin kaya guda 41 sun tashi daga birnin Zhengzhou na lardin Henan domin zuwa yankin tsakiyar Asiya, abin da ke nuna cewa, an dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin kasar Sin da yankunan Turai yadda ya kamata, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana kokarin kiyaye moriyar jama'arta, game da moriyar al'ummomin kasashen duniya baki daya. Duk wadannan sun shaida cewa, makarkashiyar wasu kasashe ta mayar da kasar Sin saniyar ware ba za ta cimma ba, kuma wannan tamkar abin dariya ne.

Sabbin alkaluma sun nuna cewa, ya zuwa jiya Lahadi 16 ga wata, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar numfashi wato COVID-19 a yankunan dake wajen lardin Hubei 115 ne kawai, adadin ya ragu a cikin kwanaki 13 a jere, kuma yanzu adadin mutanen da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar a wajen kasar Sin bai kai kaso 1 bisa dari na daukacin mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya ba.

Kamar yadda babban jami'in hukumar lafiya ta duniya ya bayyana, gwamnatin kasar Sin tana kokari matuka don hana yaduwar cutar daga tushe, abin da ya sa ta tafka mummunan hasara, haka kuma kokarin da take ya taimaka wajen hana yaduwar cutar zuwa sauran kasashen duniya, amma wasu kafofin watsa labarai gami da 'yan siyasar kasashen yamma suna ta baza jita-jita marasa tushe tare da yin kirari cewa, za a mayar da kasar Sin saniyar ware, wannan abun dariya ne, saboda kasashen duniya suna cudanya sosai a ko da yaushe a halin da ake ciki yanzu.

Annoba ba ta da iyakar kasa, ra'ayin mayar da kasar Sin saniyar ware ya sabawa burin al'ummomin kasashen duniya, muddin aka hada kai, aka yi watsi da duk wani tsari na nuna kiyayya, za a cimma burin ganin bayan annobar ba tare da wani bata lokaci ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China