Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko kasar Sin ta boye halin da take ciki dangane da cutar corona? Gaskiya na magana
2020-02-15 21:16:41        cri

Tarurukan manema labarai da ake shiryawa kafofi ne ga kasa da kasa wajen fahimtar halin da kasar Sin ke ciki wajen tinkarar cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haddasawa.

A yau Asabar, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira taron manema labarai a birnin Wuhan, hedkwatar lardin Hubei, inda cutar ta fi kamari. Taron dai ya yi amfani da fasahar sadarwa ta 5G wajen sada manema labarai da masu shirya taron.

 

A hakika, tun daga ranar 22 ga watan Janairun da ya gabata zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta shirya tarukan manema labarai sama da 25 don watsa labaran da suka shafi yanayin cutar. Kananan hukumomin kasar da suka hada da na lardin Hubei ma sun shirya tarukan manema labarai a kan lokaci. Baya ga haka, kasar Sin ta kuma yi ta sanar da hukumar lafiya ta duniya da kasashen da cutar ya shafa yanayin cutar, tare da raba musu sakamakon binciken da ta gudanar kan kwayoyin cutar.

Ko shugaban kasar Amurka Donald Trump ma ya bayyana a twitter cewa, Amurka na jinjina wa kasar Sin kan yadda take bayyana yanayin cutar ba tare da rufa rufa ba.

Sai dai mashawarcin fadar White House ta Amurka Lawrence Kudlow ya ce wai kasar Sin na boye yanayin da take ciki na fuskantar cutar corona. A game da wannan, darektan zartaswa mai kula da al'amuran ba zata na WHO Mike Ryan ya ce, gwamnatin kasar Sin na hada gwiwa da WHO yadda ya kamata, inda ta gayyaci masanan kasa da kasa tare da yin musayar bayanai da su, yana mai cewa kokarin da ta yi ya cancanci yabo, don haka, bai yarda da furucin Lawrence Kudlow ba. Ya ce, a halin da ake ciki, kamata ya yi masanan kasashen duniya su hada kansu maimakon siyasantar da batun cutar.

 

 

Wani labari na daban ya shaida yadda kasar Sin ke hada gwiwa da kasa da kasa ba tare boye komai ba. Babban darektan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a jiya cewa, ayarin masanan kasa da kasa zai isa kasar Sin a karshen wannan mako, don taimaka wa kasar tinkarar cutar.

Ko kasar Sin ta boye halin da take ciki dangane da cutar corona? Gaskiya na magana.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China