Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron nahiyar Afrika kan samar da ruwan sha da tsafta a Uganda
2020-02-25 11:40:51        cri
Masana kan harkar samar da ruwa da tsafta daga kasashen Afrika, sun fara wani taron yini 4 a jiya, domin musayar ra'ayi kan yadda za a gaggauta samar da ruwan sha da tsafta, wadanda ke zaman manyan kalubale a nahiyar.

Taron kungiyar samar da ruwa ta Afrika(AFWA) karo na 20, mai taken "sabbin dabarun samar da ruwa da tsafta ga kowa a Afrika" shi ne mafi girma a wannan bangare a nahiyar.

Yayin taron, masana za su tattauna kan sabbin dabaru da hadin gwiwa tsakanin kasashe da dai sauransu, a wani yunkuri na magance kalubalen da ake fuskanta a nahiyar a fannin samar da ruwan sha da kuma tsafta.

Kungiyar AFWA ta kunshi kungiyoyin kwararru da kamfanoni da cibiyoyi masu ruwa da tsaki a bangaren samar da ruwan sha da tsafta da muhalli a Afrika. Tana kuma da mambobi sama da 100 daga kasashe sama da 40 na fadin nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China