Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon fadan kabilanci ya tilastawa 'yan DRC sama da 300 gudu zuwa Uganda
2020-01-03 09:18:23        cri
Kwamishinan gundumomin Kikuube da Hoima dake yammacin kasar Uganda Samuel Araali Kisembo, ya bayyana cewa, sama da mutane 300 daga Jamhuriyar demokiradiyar Congo mai makwabtaka da kasar Uganda ne suka gudu zuwa cikin kasar a watan da ya gabata, sakamakon wani sabon fadan kabilanci da ya barke a lardin Ituri dake gabashin kasar ta Congo.

Samuel Arrali Kisembo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarain Xinhua ta wayar tarho cewa, mutanen sun bi ta tafkin Albert da kasashen biyu ke amfani da shi. Ya ce, suna aiki tare da jagororin yankin, da ofishin firaminista da babban kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na MDD, don kai wadannan mutane zuwa cibiyoyin tsugunar da masu kaura dake Sebigoro, duba da yadda ake sa ran Karin mutane za su tsallaka zuwa kasar ta Uganda.

A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD, kasar Uganda ita ce kasa ta uku a duniya wajen karbar 'yan gudun hijira. Inda yanzu haka kusan 'yan gudun hijira miliyan 1.36 galibi daga kasashen Sudan ta kudu, da Jamhuriyar demokiradiyar Congo(DRC), da Burundi suke samun mafaka a kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China