Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabbin mutanen da suka warke daga COVID-19 sun dara yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar cikin kwanaki shida a jere
2020-02-24 11:32:10        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin sabbin mutanen da suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19 aka kuma sallame su daga asibiti, ya dara yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a cikin kwanaki shida a jere.

Rahotanni na cewa, jiya Lahadi, an sallami mutane 1,846 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, adadin da ya dara yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a ranar, wato mutane 409.

Hukumar ta ce, ya zuwa Jiya, baki daya an sallami marasa lafiya 24,734 daga asibiti, bayan sun warke daga cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China