Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitanci da magungunan gargajiya na kasar Sin sun bada gudunmawa wajen yaki da cutar COVID 19
2020-02-23 16:54:11        cri

Mataimakin ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Xu Nanping ya bayyana a gun taron manema labarai da majalisar gudanarwa ta yi a kwanan baya cewa, Likitanci da magungunan gargajiya na kasar Sin sun bada gudunmawarsu wajen hana wadanda suka kamu da cutar COVID 19 fadawa cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Hukuma mai kula da likitanci da magungunan gargajiya ta kasar Sin ta bada kididdiga cewa, an baiwa wadanda suka kamu da cutar har ya kai dubu 60 magungunan gargajiya, tare da samun ci gaba a mataki-mataki, hakan ya sa, likitanci da magundunan gargajiya na kasar Sin sun kara shiga aikin bada jinya a fannoni daban-daban, har an ce, hada fasahohi da kimiyyar gargajiya ta kasar Sin da na zamani tare zai bada gudunmawa sosai wajen yaki da cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China