Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayyana rahoton sabbin mutane 648 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 97 sun mutu
2020-02-23 15:52:30        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa ta samu rahoton sabbin mutane 648 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, kana sabbin mutane 97 sun mutu a sanadiyyar cutar a ranar Asabar daga larduna 31 da jihar Xinjiang.

Daga cikin adadin wadanda suka mutu, 96 daga lardin Hubei ne sai mutum guda daga lardin Guangdong, a cewar hukumar lafiyar ta kasar Sin.

An samu sabbin mutane 882 da ake zaton suna da alamun kamuwa da cutar a ranar Asabar, in ji hukumar.

Kazalika a ranar Asabar din, an sallami mutane 2,230 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, yayin da aka samu raguwar mutane 509 na yawan mutanen da suke cikin matsanancin halin cutar wanda a yanzu yawansu ya koma 10,968.

Ya zuwa ranar Asabar, baki daya mutane 76,936 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a duk fadin kasar Sin, yayin da mutane 2,442 suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar numfashin ta COVID-19. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China