Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta cimma nasarar harbar tauraron dan Adam na Gaofen-10 cikin sararin samaniya
2019-10-05 16:36:07        cri
A yau ne, Sin ta cimma nasarar harbar tauraron dan Adam samfurin Gaofen-10 cikin sararin samaniya ta hanyar roka ta Changzheng-4C, tauraron ya shiga hanyar tafiya bisa shirin da aka tsara.

Tauraron dan Adam na Gaofen-10 tauraro ne da Sin ta yi nazari don yin bincike kan duniyar kasa mai inganci, za a yi amfani da shi a fannonin yin bincike kan yankunan kasa, da tsara shirin raya birane, da tsara hanyoyin motoci, da yin hasashen yawan amfanin gona da za a samu, da magance da yaki da bala'i da sauransu, hakan zai tabbatar da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da tsarin kiyaye tsaron kasa.

Kwalejin nazarin fasahohin sararin samaniya na Shanghai mai mallakar kamfanin fasahohin sararin samaniya na Sin ya yi nazarin tauraron dan Adam na Gaofen-10 da rokar Changzheng-4C.

Wannan ne karo na 314 da rokar samfurin Changzheng ta yi tafiya tare da tauraron dan Adam. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China