Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fara komawa bakin aiki yayin yaki da cutar COVID-19
2020-02-22 21:43:30        cri

Annobar cutar COVID-19 da ta bulla ba zato ba tsammani ta illata yadda ake tafiyar da harkokin zamantakewar al'umma da na tattalin arziki na kasar Sin, baya ga haddasa damuwar kasa da kasa kan karuwar tattalin arzikin Sin. Ana iya cewa, duk duniya na zura ido kan saurin farfado da ayyukan tattalin arzikin kasar.

A ranar 21 ga wata, babban daraktan kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya kira taron hukumar siyasa na kwamitin, inda ya nuna cewa, ya kamata a inganta bude kofa ga waje da hada kai da kasashen ketare, da ma kara cudanyar abokan cinikayya, baya ga tabbatar da maido da ayyukan samar da kayayyakin da za su ba da muhimmin tasiri ga aikin samar da kayayyaki na duniya da wuri, har ma da mara bayan muhimman masana'antu wajen komawa bakin aiki da wuri.

Yayin da ake ci gaba da dakile yaduwar cutar, ana fuskantar dimbin wahalhalu wajen dawo da aikin samar da kayayyaki. Domin sassauta matsin lambar kamfanoni a fannin kudin kashewa, gwamnatin kasar Sin ta fitar da jerin matakan rage yawan harajin da kudin inshorar zaman al'umma da za a karba. Sabo da wadannan manufofin da abin ya shafa, an fara komawa bakin aiki yadda ya kamata a wurare daban daban na kasar.

Dalilin da ya sa Sin ta yi hakan shi ne, ba kawai domin bunkasuwar kamfanoninta ba, har ma don kiyaye tafiyar da harkokin masana'antu na duniya yadda ya kamata. Duniya na bukatar kayayyakin da Sin ta kera, haka ma tana bukatar yadda kamfanonin Sin ke tafiyar da harkokinsu yadda ya kamata. Muddin kasar Sin, wadda ta kasance kamar wani inji mai matukar girma ta fara aiki, to aikin samar da kayayyaki da hidima na duk duniya zai iya samun tabbaci.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China