![]() |
|
2020-02-18 21:05:56 cri |
A yau da yamma ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaran aikinsa na kasar Faransa Emmanuel Macron bisa gayyatar da aka yi masa, inda ya bayyana cewa, yayin da Sin take kokarin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, shugaba Macron ya sake buga waya da nuna kulawa da goyon baya ga kasar Sin, wanda ya shaida zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Faransa da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu, don haka shugaba Xi Jinping ya gode da kuma yaba masa
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana da karfin sa kaimi ga jama'a wajen tinkarar batun kiwon lafiya na al'umma, tilas za a cimma nasarar yaki da cutar. A halin yanzu, an samu nasarori kan matakan magance da yaki da cutar. Ya ce, ya kamata a nuna goyon baya ga farfado da ayyukan kamfanoni da hukumomi yayin da ake gudanar da ayyukan magance da yaki da cutar don tabbatar da samar da kayyayakin da al'umma ke bukata. Ya ce, annobar ta yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin a wannan lokaci, ya yi imani cewa, bayan da aka yi kokari, za a cimma burin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar a bana yadda ya kamata.
A nasa bangare, Macron ya sake nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta wajen yaki da cutar, ya kuma yabawa kasar Sin kan managartan matakan da ta dauka. Ya bayyana cewa, kasar Faransa ta riga ta samar da gudummawar kayayyakin jinya ga kasar Sin, kana tana son ci gaba da ba da taimako. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China