Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya baiwa ROK tabbacin cewa, tasirin COVID-19 kan tattalin arziki da alakar kasashen biyu na kankanin lokaci ne
2020-02-20 20:34:30        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da tabbacin cewa, tasirin annobar COVID-19, na dan kankanin lokaci ne, kuma kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta na dakile tasirinta, kuma za ta zage damtse wajen ganin ta cimma nasarar manufofin da ta sanya gaba a fannonin jin dadin jama'a da tattalin arziki.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in yau Alhamis. Ya kuma yi masa bayani game da matakan kandagarki da kasar ta Sin ta ke dauka, Xi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ta dauki managartan matakai, masu tsauri da suka dace tun lokacin da wannan annoba ta barke.

Xi ya kuma lura da cewa, an samu sakamako masu gamsarwa, a yakin da kasar take yi da cutar numfashi ta COVID-19, kuma kasar Sin tana da tabbaci da ma karfin yakar wannan annoba.

A nasa jawabin, shugaba Moon, ya yaba kalaman na Xi, da ma namijin kokarin da kasar ta Sin ta ke yi na yaki da kwayar cutar. Ya bayyana tabbacin aikin kandagarki na kasar Sin, yana mai jaddada cewa, Koriya ta Kudu za ta goyi bayan kasar Sin, kana a shirye kasarsa ta ke ta yi amfani da wannan dama, wajen karfafa alaka da Sin a fannonin lafiya da ma bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China