Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna ta wayar tarho da firaministan Birtaniya
2020-02-18 20:46:07        cri

A yau da yamma ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson bisa gayyatar da aka yi masa.

Yayin zantawar, shugaba Xi Jinping ya nuna godiya ga sarauniyar kasar Birtaniya Elizabeth II da firaministan kasar Johnson bisa kulawar da suka nunawa Sin wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Birtaniya ta baiwa kasar Sin kayayyakin yaki da cutar, wannan ya shaida zumuncin dake tsakanin kasashen biyu da jama'arsu.

Xi Jinping ya jaddada cewa, bayan bullar cutar, Sin ta dora muhimmanci ga tsaron rayuka da lafiyar jama'a, da yin amfani da fifikonta na tsari, da yin kokari tare wajen daukar matakan magance da yaki da cutar a dukkan fannoni. Bayan wadannan matakai da aka dauka, yanzu an samu nasara a yakin da ake yi da wannan cuta. A halin yanzu, an shiga lokaci mafi muhimmanci kan aikin, don haka ya kamata a yi kokarin rage tasirin da cutar ta haifar yayin da ake yin kokarin magance da ma yaki da cutar.

A nasa bangare, Johnson ya nuna yabo ga kasar Sin kan matakai masu tsauri da suka dace da ta dauka na magance da yaki da cutar, da ma kokarin hana yaduwar cutar a duniya. Ya yi imani da cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, babu shakka jama'ar kasar Sin za su cimma nasarar yaki da cutar, da rage tasirin da cutar za ta haifar wa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China