Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban babban bankin jama'ar Sin: Illar da annobar COVID-19 ke yi wa tattalin arzikin kasar ba zai shafi lokaci mai tsawo ba
2020-02-22 15:48:50        cri

Mataimakin shugaban babban bankin jama'ar kasar Sin, Chen Yulu, ya bayyana cewa, illar da annobar COVID-19 ke yi wa tattalin arzikin kasar, na kankanin lokaci ne, kuma bai shafi dukkan fannoni ba, yana mai cewa, tsarin hada-hadar kudin Sin na da matukar karfin tinkarar hadari.

Mr. Chen ya yi wannan furuci ne yayin da yake zantawa da wakilin babban gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG, a jiya Juma'a. Ya kara da cewa, babu shakka annobar ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar Sin, amma bisa kyawawan sakamakon da kasar ta samu wajen dakile yaduwar cutar, wanda ya zarce zaton kasashen duniya, ana iya hasashen cewa, yadda tattalin arzikin kasar ke dada karuwa da samun ci gaba mai inganci cikin dogon lokaci, ba zai sauya ba.

Ban da wannan kuma, Mr. Chen ya bayyana cewa, ba tare da bata lokaci ba, bayan bullar cutar, babban bankin ya samar da rancen kudi Yuan biliyan 300 domin tallafawa kamfanonin da ke ba da gudummawa ga aikin yaki da cutar, baya ga hada kai da ya yi da hukumomin da abin ya shafa wajen fitar da matakai 30 na goyon bayan aikin yaki da cutar, lamarin da ya samu jinjina daga asusun ba da lamuni na duniya da sauran takwarorinsa na duniya.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China