Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da tattaunawa da Japan kan yaki da COVID-19
2020-02-21 20:47:45        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da tattaunawa da ma yin hadin gwiwa da kasar Japan kan yadda za a tabbatar da tsaro da kare rayukan al'ummomin kasashen biyu, da ba da gudummawa a kokarin da ake na samar da tsaron lafiya a shiyya da duniya baki daya.

Geng shuang ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai ta kafar Intanet, lokacin da yake mayar da martani kan tattaunawar da kasashen Sin da Japan suka yi game da yaki da wannan annoba. Ya ce, a matsayinsu na kasashen dake makwabtaka da juna, Sin da Japan za su hada kai wajen ganin bayan wannan annoba.

Ya ce, a lokacin da cutar ta bulla, gwamnati da al'ummar Japan sun baiwa kasar Sin tallafi da goyon baya a lokacin da ya dace, kuma kasar Sin ba za ta manta da wannan abokantaka ba. Al'ummar Sinawa suna sa-ido da ma nuna damuwa kan yanayin wannan annoba a kasar Japan, kuma Sin na tare da Japan kan halin da ta ke ciki.

Jami'in ya ce, a lokacin da muka taimakawa juna, wannan shi ne abokanta da amincewa da juna, kuma wannan shi ne yadda kasar Sin da sauran al'ummomin kasa da kasa ke tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta cikin hadin gwiwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China