Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci dakarun sojin Sudan ta Kudu da su kauracewa yankunan fararen hula
2020-02-06 11:41:06        cri
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta yi kira ga dakarun soji da na tsaron gwamnatin Sudan ta Kudu, da su gaggauta ficewa daga yankunan fararen hula da suka mamaye ba bisa ka'ida ba.

Cikin wata sanarwa, majalissar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar AU, ta yi kira ga dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu, da su janye daga yankunan fararen hula 25 ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kaza lika majalisar ta gargadi dakarun da su kauracewa daukar dukkanin wasu matakai, da ka iya karya dokokin kasa da kasa. Ta ce watsi da wannan kira, zai iya jawo kakaba takunkumi kan dukkanin masu hannu a aikata hakan.

Majalissar ta yi kiran ne cikin wata takardar bayan taro a jiya Laraba, bayan kammala zaman tattaunawar baya bayan nan, game da yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu.

Bugu da kari, majalissar ta nuna matukar damuwa, game da kara tabarbarewar yanayin jin kai a kasar. Jami'an majalissar sun kuma yi kira ga kasashe mambobin kungiyar ta AU, da ma sauran abokan hulda na kasa da kasa, da su samar da kayayyakin da ake tsananin bukata, da tallafin kudade, da za a yi amfani da su wajen rage radadin halin da fararen hula ke ciki a Sudan ta Kudu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China