Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Rasha ya sanar da murabus din gwamnatin kasar
2020-01-15 22:53:39        cri

Rahotanni daga kafofin watsa labaran kasar Rasha sun ce, firaministan kasar Dmitry Medvedev ya sanar da murabus din gwamnatin kasar.

A cewar Dmitry Medvedev, a cikin rahoton da shugaba Putin ya gabatar ga majalisar dokokin kasar, ya bayyana wasu abubuwan da suka shafi yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul, abun da zai yi babban tasiri ga daidaiton iko gami da bangarorin mulki da kafa doka da shari'a da sauransu bayan da aka amince da shi. A sabili da haka, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta Rasha ta baiwa shugaban kasar duk wata damar da zai yanke sharawa. Medvedev ya ce, bisa tanadi na 117 na kundin tsarin mulkin kasar, ya kamata gwamnati ta yi murabus.

Shugaba Putin ya kuma bayyana niyyarsa ta kara wani gurbin aiki na mataimakin shugaban taro kan harkokin tsaro na tarayyar Rasha, da gabatar da sunan Medvedev don ya kama aikin. Putin ya godewa gwamnatin kasar ta yanzu saboda ayyukan da ta yi, tare da bukatar dukkan membobin gwamnatin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kafin a kafa sabuwar gwamnati.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China