Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manoman kasar Kenya sun shiga rudani sakamakon karatowar damuna mai tattare da matsaloli
2020-02-20 13:03:35        cri

Manoman kasar Kenya sun shiga rudani, sakamakon karatowar damuna mai tattare da tasirin yanayi, da farin dango dake addabar sassan kasar.

Da yake tsokaci game da hakan, wani manomin masara a yankin Kitale dake yammacin kasar mai suna George Ambuche, ya ce a shekarun baya a irin wannan lokaci ne ake fara ayyukan gona.

Ya ce ya zuwa watan Maris na ko wace shekara ayyuka sun kankama, amma a wannan shekara kusan kwanaki 10 suka rage a shiga watan na 3, amma manomin, da ma sauran mutane masu sana'a irin ta sa, ba su ko fara shiri ba. Ya ce " Muddin ban ga saukar ruwan sama ba, ba zan yi hudar gona ta ba."

Ambuche ya ce, a bara, ya yi asarar kudi masu yawa da takin zamani, da hayar motar noma, da irin shuka wanda daga baya sai da ya sake yin shuka saboda jinkirin saukar ruwan sama. Ya ce ba zai sake yin hakan ba, domin an shani na warke. Wannan dai shi mataki da mafiya yawan manoman kasar ke dauka.

Wannan matsala ce da ta shafi dubban manoma a sassan gabashin Afirka, yayin da kasashe irin Kenya ke fuskantar mummunan tasirin yanayi. Halin rashin tabbas, ya jefa miliyoyin manoma cikin halin tsaka mai wuya, duba da cewa mafi yawan su, na dogaro ne da ruwan sama domin gudanar da sana'ar su. A cewar Macharia, sauyin yanayi ya haifar da bullar tsutsotsi ,da farin dango dake cinye amfanin gona, wanda hakan ya kara tsananta halin da manoman ke ciki.

A cewar hukumar abinci da aikin gona ta MDD, a halin da ake ciki, Kenya na fama da farin dango wadanda cikin shekaru 70 ba a taba ganin munin barnar da ta kai wadda suke yi a halin yanzu ba.

Da yake tsokaci game da hakan, ministan ma'aikatar gona ta kasar Peter Munya, ya ce cikin watanni 2 da suka gabata, an yi ta yunkurin dakile wadannan fari, amma har yanzu ba a cimma cikakkiyar nasara ba. Don haka a ranar Litinin din farkon makon nan, ya yi kira ga daukacin al'ummar Kenya, da su kara hakuri da matakan da gwamnati ke dauka, na feshin magungunan kashe farin ta kasa da sama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China