Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi hasashen tattalin arzikin Kenya zai karu da kashi 6.1 a 2020
2020-01-23 11:46:51        cri
Hasashen da hukumar kula da baitilmalin kasar Kenya ta fitar ya nuna cewa tattalin arzikin kasar zai karu da kashi 6.1 bisa 100 a shekarar 2020, inda zai iya zarce kashi 5.6 bisa dari na shekarar 2019.

Babban sakataren hukumar adana kudaden kasar Ukur Yatani, ya bayyana cewa, za'a samu bunkasuwar ne ta hanyar ayyukan hidima na sauran fannoni, da samar da muhallin daidaita kananan sana'o'i, da ci gaba da aiwatar da dabarun zuba jari wanda gwamnatin kasar ke baiwa fifiko karkashin wani shiri na "Big Four Agenda" wato manyan ajandodi hudu.

Yatani ya ce, shekarar da ta gabata, daya daga cikin dalilan da suka haifar da koma bayan ci gaban tattalin arzikin kasar shi ne rashin samun ruwan sama a cikin watanni shidan farko na shekarar 2019, lamarin da ya haifar da illa ga fannin aikin gona.

A cewar bayanan dake kunshe cikin manufofin kasafin kudin kasar na shekarar 2020 wanda aka fitar kwanan nan, a cikin gidan kasar, tattalin arzikin kasar zai ci gaba da fuskantar barazana daga bangaren kudaden da gwamnati ke kashewa a kasafin kudi na ayyukan yau da kullum, musamman daga fannin kudaden albashin da ake biya ma'aikata da matsalar sauyin yanayi wanda ba za'a iya kauce masa ba dake haddasa wasu bala'u kamar zaftarewar kasa, da fari, gami da lalata wasu muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China