Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kasashen Afirka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar dinke manufofin shige da fice
2020-01-22 10:26:05        cri
Ministocin kwadago na kasashen gabashi da kahon Afirka, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya, wadda ta tanaji hade manufofi da ka'idojin shige da fice na kasashensu.

Ministocin sun amince da wannan yarjejeniya ne, yayin taron yini biyu da suka gudanar a birnin Nairobin kasar Kenya, da nufin karfafa tsaro, da inganta bin dokokin kwadago tsakanin kasashen, ta yadda za su dace da mizanin shiyyoyi da na kasa da kasa.

Da yake karin haske bayan kammalar taron, sakatare a ma'aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ta kasar Kenya Simon Chelugui, ya bayyanawa 'yan jarida cewa, "Mun amince da aiwatar da ka'idojin yanki da na kasa da kasa, wadanda suka yi tanadin samar da 'yancin zirga zirga, don fadada damar samar da guraben ayyukan yi, da dakile fasa kwauri, da safarar bil Adama, da bautar da mutane".

Ministoci mahalarta taron dai sun fito ne daga kasashen Kenya, da Uganda, da Tanzania, da Somalia, da Habasha. Sauran sun hada da na Sudan ta kudu, da Eritrea, da Djibouti, da Rwanda da kuma Burundi. Yayin taron, sun kuma amince da tura wakilan musamman na harkonin kwadagon kasashensu zuwa kasashen juna, domin samar da kariya ga 'yan kasashen su bisa doka, a fannin 'yancin bil Adama, da ayyukan 'yan ci rani, duka dai da nufin dakile cutarwar da al'ummunsu mazauna ketare ke fuskanta, da tabbatar da bin doka da oda tsakanin al'ummun ko wane bangare. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China