Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurkawa 3 sun mutu a sakamakon harin da aka kai a sansanin soja na Kenya
2020-01-06 11:15:11        cri
Bangaren soja na kasar Amurka ya bayyana a jiya cewa, wani soja guda, da masu samar da kayayyaki ga ma'aikatar tsaron kasar Amurka guda biyu sun mutu, a sakamakon harin da wasu dakaru suka kai a wani sansanin soja da ke kasar Kenya a wannan rana.

Ofishin kwamanda mai bada umurni na kasar Amurka dake nahiyar Afirka ya bayar da sanarwar cewa, ban da wadannan Amurkawa 3, akwai sauran wasu jami'an ma'aikatar tsaron kasar Amurka biyu da suka samu raunuka a sakamakon harin.

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin kiyaye tsaron kasar Kenya, da ofishin kwamandan Amurka dake Afirka sun cimma nasarar dakile harin da kungiyar Al-shabaab ta kasar Somaliya ta kaddamar.

Bangaren soja na kasar Kenya ya bayyana a wannan rana cewa, kungiyar Al-shabaab ta kasar Somaliya, ta kai hari wani sansanin soja mallakar sojojin Kenya da Amurka, dake garin Lamu na kasar Kenya. Daga baya, bangaren soja na Kenya da masu kai harin sun yi musayar wuta, inda aka harbe dakaru 5 har lahira.

Kakakin sojojin tsaron kasar Kenya Paul Njuguna, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, da karfe 5 da rabi na yammacin jiya, dakarun sun kunna wuta, da yunkurin lalata hanyoyin filin jiragen sama na sansanin. Daga baya, bangaren soja na Kenya da dakarun sun yi musayar wuta. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China