Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firayin ministan Sin ya kira taron dakile cutar numfashi
2020-02-17 21:06:18        cri
Yau Litinin firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya shugabanci taron karamar kungiyar jagorancin aikin dakile cutar numfashi ta COVID-19 ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda aka bayyana cewa, aikin hana yaduwar cutar ya samu ci gaba matuka, yanzu haka birnin Huhan da sauran biranen lardin Hubei sun fi shan wahalar yaduwar annobar, don haka ya dace a kara mai da hankali kan wuraren, kana an yi nuni da cewa, yayin da ake kokarin dakile annobar, akwai bukatar sanya lura ga batun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.

Yayin taron, an jaddada cewa, dole ne a kara karfafa aikin tantance mutanen da ake zaton sun kamu da cutar a birnin Wuhan da biranen dake fadin lardin Hubei, tare kuma da samar musu da karin gadajen jinya, haka kuma gwamnatin kasar za ta kara tura ma'aikatan jinya zuwa wuraren domin ba su kulawa, ta yadda za a ceto rayukan wadanda cutar ta yi tsanani a jikinsu, a sa'i daya kuma, ya zama wajibi a tabbatar da lafiyar ma'aikatan jinya, tare kuma da samar musu isassun kayayyaki da na'urorin da suke bukata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China