Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya isa Wuhan domin duba ayyukan yaki da cutar numfashi ta coronavirus
2020-01-27 20:23:21        cri
Bisa yardar babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, firaministan kasar Li Keqiang ya isa birnin Wuhan na tsakiyar kasar Sin a yau Litinin, domin aikin sanya ido ga matakan da ake aiwatarwa, na kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi da ake fama da ita.

Li Keqiang dai na jagorantar tawagar kwamitin JKS, wadda aka dorawa nauyin tabbatar da ana aiwatar da managartan matakan kandagarki, da dakile yaduwar cutar, wadda kwayoyin cutar coronavirus ke haddasawa.

A birnin na Wuhan, Li, wanda kuma mamba ne a zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya jinjinawa jami'an lafiya dake aiki tukuru wajen lura da marasa lafiya, ya kuma yi kira gare su, da su dora muhimmancin gaske ga kare kansu.

Kazalika firaministan na Sin, ya jaddada bukatar tabbatar da ana samar da isassun kayan kula da lafiya, a kuma yi aikin jinyar wadanda suka kamu da cutar cikin gaggawa, da samar da kayayyakin da ake da bukatar amfani da su a kasuwanni bisa farashin da ya dace.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China