Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya buga waya ga shugabar gwamnatin kasar Jamus
2020-02-10 10:34:27        cri

Firaministankasar Sin Li Keqiang ya buga waya ga shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel a daren jiya bisa gayyatar da aka yi masa, inda suka yi musayar ra'ayoyi game da ayyukan yaki da cutar coronavirus.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, gwamnatin kasar Sin tana gudanar da ayyukan magance yaki da cutar bisa dokoki da kimiyya da fasaha, da yin kokarin ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar, da kuma tabbatar da samar da kayayyakin kiwon lafiya da na zaman yau da kullum da ake bukata. Gwamnatin kasar Sin ta ba da muhimmanci ga tsaron rayuwa da lafiyar al'umma. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna da imani da karfi wajen cimma nasarar yaki da cutar.

A nata bangare, Merkel ta bayyana cewa, kasarta ta Jamus tana mayar da hankali sosai kan yanayin yaki da cutar. Ta ce gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai cikin sauri, wadanda suka samu goyon baya daga jama'arta. Kasar Jamus tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen magance da yaki da cutar, da ci gaba da samar da gudummawar kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata don taimakawa kasar Sin wajen cimma nasarar yaki da cutar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China