Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya tattauna da shugabar kwamitin hukumar EU
2020-02-01 16:29:14        cri
Bisa gayyatar da aka yi masa Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tattauna ta wayar tarho da shugabar kwamitin hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, inda Li Keqiang ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin tana sanya tabbatar da lafiyar jama'a gaban komai, kana tana gudanar da ayyukan yaki da cutar numfashi da ta bulla a kasar yadda ya kamata. Ya ce aiki mafi muhimmanci da ake gudanarwa a halin yanzu shi ne, dakile yaduwar cutar, da jinyar wadanda suka kamu da ita, da kuma tabbatar da yanayin rayuwar jama'ar kasar da ma wadanda ke rayuwa a kasashen waje yadda ya kamata.

Li Keqiang ya jaddada cewa, ana kokari wajen tabbatar da samar da kayayyakin aikin jinya, kuma yana fatan kungiyar EU za ta samarwa Sin sauki wajen sayen wadannan kayayyaki daga kasashe membobinta.

A nata bangare, Von der Leyen ta bayyana cewa, kungiyar EU tana girmamawa tare da jinjinawa matakan da kasar Sin ta dauka na yaki da cutar cikin sauri.

Ta ce kungiyar EU za ta yi kokari tare da samar da albarkatu ga kasar Sin da kuma kira ga kasashe membobinta da su samar da sauki ga Sin yayin da take sayen kayayyakin kiwon lafiya daga wajensu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China