Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya yi kira da a kara azama wajen aiwatar da matakan kandagarki da na dakile yaduwar cutar numfashi
2020-01-28 15:58:45        cri

Bisa yardar babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, firaministan kasar Li Keqiang, ya isa birnin Wuhan na tsakiyar kasar Sin a jiya Litinin, domin aikin sanya ido game da matakan da ake aiwatarwa, na kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi da ake fama da ita, inda ya bukaci dukkanin jami'an lafiya da su yi duk mai yiwuwa, wajen tabbatar da dakile yaduwar cutar, a matsayin mataki mafi muhimmanci na tsayar da adadin masu rasa rayukan su, da adadin sabbin wadanda cutar ke kamawa.

Li Keqiang dai na jagorantar tawagar kwamitin JKS, wadda aka dorawa nauyin tabbatar da ana aiwatar da managartan matakan kandagarki, da dakile yaduwar cutar, wadda kwayoyin cutar coronavirus ke haddasawa.

A madadin JKS da kuma majalissar gudanarwar kasar ta Sin, Li ya gabatar da sakon gaisuwa da jinjina ga ma'aikatan dake bakin aiki a birnin na Wuhan.

Bayan isar sa birnin, Li ya ziyarci asibitin Jinyintan wanda ke dauke da adadi mafi yawa na masu dauke da cutar. Ya kuma zanta da jami'an lafiya dake lura da wadanda aka kebe ta na'urar bidiyo. Kaza lika ya tattauna da likitoci da jami'an jinya, da ma sojojin dake aikin tallafawa yaki da cutar, yana mai fatan za su yi namijin kokari a wannan muhimmin aiki, tare da tabbatar da sun kare kawunan su. Daga nan sai ya umarci da a tura karin jami'an lafiya, musamman ma masu aikin jinya, da tura karin kayan aikin kiwon lafiya zuwa Wuhan.

Har ila yau, ya bukaci a kara hanzarta aikin gina sabon asibitin Huoshenshan da ake kan aikin sa, wanda aka tsara samarwa musamman domin lura da masu dauke da wannan cuta a yankin.

Da yake tsokaci ga jama'ar da ya zanta da su a wani shagon sayar da kayan masarufi, firaministan ya ce kasar Sin na da albarkatu, da tsarin samar da abinci, wanda zai ba da damar samar da isassun abubuwan bukata na yau da kullum kan farashi da ya dace a birnin na Wuhan.

Li ya kuma ziyarci wani dakin gwajin cututtuka da hana yaduwar su na lardin Hubei, inda ya bukaci ma'aikatan sa da su kara azama, wajen gano matakan magance cutar ta coronavirus.

A wani bangaren kuma, Mr. Li ya kira wani taro, domin zurfafa tattaunawa game da matakan kandagarki, da na dakile yaduwar wannan cuta da ta bulla, a mataki na bincike, da na kebe muhimman wurare mafiya hadari, yana mai cewa, nasarar da za a samu a Wuhan, za ta karfafa zukatan al'ummar kasar baki daya.

Ya ce za a tallafawa birnin Wuhan da karin jami'an lafiya 2,500, da kuma gilasan kare idanu 20,000 (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China